Erdogan ya yi wa gwamnatinsa gyara

Recep Tayyip Erdogan
Image caption Recep Tayyip Erdogan

Pirai ministan Turkey Recep Tayyib Erdogan ya bayyana sunayen sababbin ministoci 10 a wani garanbawul da ya gudanar a gwamnatinsa.

Wannan yunkuri ya biyo bayan murabus din da wasu ministoci uku suka yi wadanda aka kama 'ya'yansu sakamakon wani binciken cin hanci da rashawa da aka yi.

Wakilin BBC a Istanbul ya ce garambawul din wani yunkuri ne na Pirai minista Erdogan ya tabbatar da ikonsa a karshen shekarar da ya yi fama da rikici.

A baya bayan nan dai an yi ta gudanar da zanga-zangar rashin goyon bayan gwamnatin Mr Erdogan a Istanbul da sauran manyan biranen Turkey.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba