China na bikin shekaru 120 da haifar Mao

Kabarin Mao Zedong na karbar manyan baki
Image caption Kabarin Mao Zedong na karbar manyan baki

Ana gudanar da bukukuwa a China na shekaru 120 da haihuwar Mao Zedong, wanda ya kafa kasar China ta wannan zamani.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce manyan shugabannin China, ciki har da shugaban jam'iyyar gurguzu, Xi Jinping sun kai ziyarar ban girma kabarin Mao dake Beijing.

Jaridar jam'iyyar ta ce babbar girmamawar da za'a yi wa Mao ita ce ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki koda yake sai bayan mutuwarsa aka kaddamar da su.

Masu aiko da rahotanni sun ce 'yan siyasar China na kokarin daidaita yabon Mao saboda kirkiro tsarin siyasar kasar da kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin manufofinsa sun gama yayi.