Shekaru 120 da haihuwar Mao Zedong

Image caption Mao Zedong ne ya kafa kasar China ta zamani.

Kasar China na gudanar da bukukuwan shekaru 120 da haihuwar Mao Zedong wanda ya jagoranci juyin juya halin kasar.

Shekaru 37 bayan mutuwarsa, kawo yanzu Mao Zedong na cigaba da janyo cece -ku ce- kamar lokacin rayuwarsa.

Marigayin ya rika fafutukar yaki da mulkin mallaka, da danniya da kuma akidar nan ta jari huja a kasar China da kuma sauran kasashen duniya.

Ko da yake manufofinsa sun haifar da rikici tsakanin jam'iyyu kuma masu sharhi sun ce hakan ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin 'yan kasar China.

Dangantaka da Afrika

Marigayi Mao Zedong ya goyi bayan fafutukar da 'yan kasashen Afrika suka rika yi akan mulkin mallaka, abin da kuma ya sa ya kulla kawance da wasu shugabanin kasashen Afrika, ciki har da shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda , da shugaban kasar Tanzania Juluis Nyerere da kuma Shugaba Musa Traore na kasar Mali.

A wancan lokaci marigayin ya yabawa kokarin da mutanen suka yi wajen samawa kasashensu 'yanci daga turawan mulkin mallaka.

Lokacin da shugaba Julius Nyerere na Tanzania ya ziyarci China a 1965 ya nemi taimakon Mr Mao wajen gina layin dogo a kasarsa, abinda Mao ya amince.

A shekarar 1975 aka kammala layin dogo akasar Tanzania da tallafin da China ta bayar tare kuma da maikata masu dimbin yawa inda 66 daga cikinsu suka mutu lokacin aikin gina layin dogon.

Image caption Julius Nyerere na Tanzania ya kulla alaka da Mao Zedong

Farfesa Stephen Chan masanin kimiyar Siyasa, ya ce tsare tsaren marigayi Mao sun fi jan hankalin shugabanin Afrika na wancan lokaci

Ya ce: "Chairman Mao mutum ne da shugabannin Afrika na wancan lokaci ke girmamawa, saboda bai bambanta tsakaninsu ba, sabanin abin da a wasu lokutan shugabannin kasashen Turai ko Amurka ke nuna masu."

Majalisar Dinkin Duniya

Hadin kan dake tsakanin China da nahiyar Afrika ne ya sa China ta samu kujera a Majalisar Dinkin Duniya a 1971 bayan kasashen Afrika 27 da kuma wasu kasasahen duniya 49 sun kada kuriar amincewa China ta samu kujera a majalisar duk da cewa kasa ce mai bin tafarkin kwaminisanci.

Haka kuma kasashen Afrika sun yi ta turawa da sakonnin ta'aziyya lokacin da chairman Mao ya mutu a shekarar 1976.

Shugaba Moktar Dadaah na kasar Mauritania ya kira maragayin kwararre a harkar siyasa, shi kuma shugaba Yakubu Gowon na Najeriya ya yabawa hangen nesan marigayin kuma ya ce ba za'a taba mantawa da shi ba a tarihin duniya.

Image caption Yakubu Gowon na Nigeria ya ce ba za'a manta da Mao ba.

A yanzu dai sababbin shugabbani ke mulki a nahiyar Afrika, inda akwai wasu da suka cigaba da karfafa dagantakar dake tsakaninsu da China yayin da wasu kuwa sun fi mai da hankali ne wajen karfafa hulda da kasasahen yamma.

To ko ya marigayi Mao zai ji akan halin da nahiyar Afrika ke ciki yanzu?

Ga dai abin da Farfesa Chan ke cewa: "Abin da ke faruwa ba zai ba Mao mammaki ba ko dayake watakila jarin hujja da ya shigo ciki ya bashi mamaki.

A yanzu China na cikin kasashen duniya masu karfin fada a ji wanda a baya kasashen yamma suka yi wa babakare.

Haka kuma Mao zai ji dadi akan yadda China da kasashen Afrika ke cigaba da karfafa alakar dake tsakaninsu da kuma abubuwan da China ke yi domin inganta rayuwar alummar Afrika."