Ba dafi ne ya kashe Arafat ba - Rasha

Image caption Matar Arafat na zargin an kashe shi ne da dafin Polonium.

Masu binciken kimiyya a Rasha da ke nazari kan gawar marigayi shugaban Palasdinawa Yasser Arafat sun ce ta Allah ce ta kasance a kansa, ba wai dafi aka sa masa ba kamar yadda matarsa ke zargi.

Sakamakon binciken na Rasha ya zo daidai da sakamakon da masana kimiyya a Faransa suka bayar.

Wasu manazarta a Switzerland sun ce sun gano dafin polonium mai dimbin yawa a jikinsa, sai dai sun ce ba zasu iya tabbatar da ko shi ne ya kashe shi ba.

A bara ne aka tono gawar Mr Arafat wanda ya mutu a 2004, inda aka ciri sassa 60 a jikinsa aka rarraba tsakanin masana a Switzerland, Rasha da Faransa.