Za'a fara sasanta rikicin Sudan ta Kudu

Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.

Jami'an gwamnatin Sudan ta kudu sun ce su na tsammanin isowar Shugaban kasar Kenya da kuma Firaministan Habasha zuwa Juba a yau Alhamis a wani bangare na cigaba da yunkurin kawo karshen fadan da ake yi a kasar.

Shugaba Salava Kiir ya ce a shirye ya ke a tattauna sai dai abokin hamayyarsa Riek Machar ya ce sai an saki wadansu gaggan magoya bayansa kafin ya amince da tattaunawar.

Har yanzu ana cigaba da gwabzawa a yankin da ke da albarkatun mai da ke arewacin kasar inda dakarun gwamnati suka samu nasarar kwato ikon wasu garuruwa.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa akwai gawawwakin jama'a akan titunan garin Bor da aka kwace ranar Talata.

Karin bayani