An fara sasanta rikicin Sudan ta Kudu

Image caption Pirai ministan Ethiopia, shugaban kasar Sudan ta kudu da shugaban kasar Kenya.

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da Pirai ministan Ethiopia, Hailemariam Desalegn sun isa Sudan ta Kudu, in da za su yi kokarin sasanta wa tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da abokan hamayyarsa.

Shugaba Kiir ya ce a shirye yake a tattauna, amma abokin hamayyarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar, ya ce sai an sako gaggan magoya bayansa kafin ya amince da tattaunawar.

Ana ci gaba da yaki a yankunan arewacin kasar masu arzikin man fetur, inda dakarun gwamnati suka karbe wasu garuruwan da 'yan tawaye suka kwace.

Bishop na Juba, Santo Loko Pio ya ce yakin da ake yi a Malakal da ke arewa maso gabashin kasar ya sa mutane sun shiga boyo maimakon bukukuwan Kirismeti.