Bom ya girgiza birnin Beirut

Image caption Bakin hayaki ya turnuke tsakiyar birnin Beirut.

Fashewar wani bom ta girgiza Beirut, babban birnin Lebanon.

Bakin hayaki ya turnuke tsakiyar birnin kusa da ofisoshin gwamnati da kuma ginin majalisar dokoki.

Rikicin Syria ya kara zafin bambance-bambancen da ke tsakanin al'umomin makwabtanta, abinda ke haddasa munanan hare-hare.

Mayaka Musulmi 'yan Sunni a Lebanon sun hada kai da 'yan tawayen Syria wadanda mafi yawansu Sunni ne.

Shugaban Syria Assad mabiyin akidar Alawi ne, wacce ta samu tushe daga Shia.

Kungiyar 'yan bindiga 'yan shia ta Lebanon, Hezbollah ta aike da mayaka su tallafawa gwamnatin Syria.

A watan jiya an kai hari a Beirut kan ofishin jakadancin Iran mai goyon bayan Hezbollah.