Rikici na kara tsananta a Afrika ta tsakiya

Image caption Rikicin Afrika ta TSakiya na kara kazanta

Amurka ta ce rikicin da ake a Afrika ta Tsakiya inda ake gwabzawa a Bangui babban birnin kasar ya tsananta lamarin da ya haddasa rasa rayukan mutane da dama.

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, ya bukaci hukumomi a Afrika ta Tsakiya da su gaggauta gudanar da zabe.

Kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce ta gano gawawwakin mutane fiye da arba'in a kan titunan Bangui babban birnin Afrika ta Tsakiya, bayan rikicin da ke cigaba da gudana a kasar.

Sojojin sa kai na Kirista sun kashe sojojin kasar Chadi shida da suke tawagar dakarun kiyaye zaman lafiya na Afrika wadanda aka tura gida saboda zargin da ake musu cewa su na marawa musulmai 'yan tawaye baya.

Mai magana da yawun kungiyar ta Red Cross ya ce fadan da ake yanzu haka a Bangui ya tsananta matuka lamarin da ya sa ma'aikatan kungiyar ta su ba za su iya kaiwa ga wasu bangarori a garin ba.

Ya ce ya na fargabar cewa an kashe mutane da dama a garin.

Karin bayani