Za a tuhumi Amadou Toure na Mali

Tounami Toure
Image caption An zarge Toure da cin amanar kasa

Gwamnatin Mali ta sanar da cewa za ta fara shirye-shiryen tuhumar tsohon shugaban kasar Amadou Toumani da laifin cin amanar kasa.

Gwamnatin ta zargi Mr. Tounami da gazawa a matsayinsa na shugaban Sojojin Mali, da ya bari 'yan tawayen Azbinawa da masu kaifin kishin Islama suka kwace iko da arewacin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa tsohon shugaban kasar ya yanyo rundunar sojin kasar ta yi rauni.

Sojojin Mali dai sun jagoranci juyin mulkin da yayi sanadiyyar hambarar da gwamnatin Mr Tounami a watan Maris din shekarar da ta gabata.

Karin bayani