'Jahohin Najeriya basa iya dogaro da kansu'

Image caption 'Jahar Legas ce kadai zata iya dogaro da kanta'

A Najeriya, wasu bayanai na nuna cewa jihohi talatin da biyar daga cikin jihohi talatin da shida na kasar ba zasu iya dogaro da kansu ba, ba tare da karbar kason wata-wata daga gwamnatin tarayya ba.

Bayanan na nuna cewa jihohin ba su iya tara kudaden shiga na cikin gida da za su ishe su biyan albashi balle a yi batun gudanar da manyan ayyuka na raya kasa.

Daya daga cikin manyan jaridun Nijeriya wato Daily Trust ta bayyana cewa a bincikenta ta gano cewa jihar Legas ce kadai ke samun kudaden shiga na cikin gida da zata iya dogaro da kanta wajen biyan albashi ba tare da samun kudade daga baitulmalin tarayya ba.

Malam Usman Dutse malamin Kimiyyar tattalin arziki ne a kwalejin kimiya da fasaha ta tarayya dake Bauchi, ya bayyana cewa son zuciya da rashin iya shugabanci shine ya janyo haka.