Za'a tattauna kawar da makaman Syria

Image caption Syria ta amince a kawar da makamanta masu guba.

Wakilai daga Rasha, Amurka, Syria da Majalisar Dinkin Duniya za su gana a Moscow da yammacin Juma'a domin tattauna yadda za'a kawar da makamai masu guba daga Syria lami lafiya.

Rasha ta aike da motoci zuwa Syria domin kwaso makaman inda za'a fitar da su daga tashar jiragen ruwa ta Latakia a cikin jiragen Norway da Denmark.

Hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba ta duniya, OPCW ta bada wa'adin kawar da makaman daga Syria nan da karshen watan nan.

Kasar ta amince ta lalata makamanta masu guba ne karkashin wata yarjejeniya da Rasha ta jagoranta domin kauce wa barazanar harin soji daga Amurka.