Binciken cinhanci a Turkiyya ya sauya salo

Image caption Ana zargin yin kafar lauje kan binciken cinhanci a Turkiyya

Wani mai gabatar da kara a Turkiya ya ce an hana masa gudanar da cikakken bincike game da zargin cin hanci a tsakanin jami'an gwamnatin Turkiya.

A cikin wata sanarwa Mu'ammar Akkas, ya ce 'yan sanda sun kawo cikas ga kokarin ta hanyar kin yin wasu kame kamen da ya umurta a yi.

Ya kara da cewar an cire shi daga binciken zargin.

Babban mai gabatar da kara na Santanbul Turhan Colakkadi, ya shaidawa Kamfanin dillanci labarai na Reuters cewar an cire shi saboda kwarmata wa kafofin watsa labarai bayanai.

A ranar Laraba ministociuku ne suka yi murabus bayan da aka kama 'ya 'yansu a wani bangare na binciken cin hanci.

Firaiministan Turkiyar Recep Tayyip Erdogan ya wani garanbawul ga majalisar zartarwa.

Karin bayani