Kasashen duniya za su ware Sudan ta Kudu

Image caption Shugabannin Afrika na tattauna rikicin Sudan ta Kudu

Ministan harkokin wajen Uganda ya ce za'a mai da Sudan ta Kudu saniyar ware tsakanin kasashen duniya idan aka ci gaba da yaki a kasar.

Mr Henry Oryem Okello ya shaidawa BBC cewa kasashen duniya za su katse huldar diplomasiyya da Sudan ta Kudu idan jagororinta suka ki bada hadin kai wurin sasanta rikicin da suke.

Ya kuma ce za'a tuhumi wadanda suke da laifin kashe-kashen da ake a kasar.

Shugabannin yankin dai na ganawa a Nairobi, babban birnin Kenya domin tsara tattaunawar sulhun.

Karin bayani