Zaben kananan hukumomi a Yobe

Zabe
Image caption Wannan shine zabe na farko a Yobe tun bayan kafa dokar- ta- baci

A yau ake gudanar zaben kananan hukumomi a jahar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumomi na cewa zaben na tafiya daidai, duk da zargin cewa a wasu yankunan ba a samu kai kayan zaben a kan lokaci ba.

Jam'iyyu goma ne ke fafatawa a wannan zaben na Shugabannin kananan hukumomi goma sha bakwai da ke Jahar.

Jam'iyyar PDP ta 'yan adawa a jihar, ta ce zata kaurace ma zaben, saboda fargabar tsaro.

Wannan shi ne zabe a karon farkon tun bayan da gwamnatin kasar ta kafa dokar -ta-baci a jahar.

Jahar ta Yobe dai na daga cikin jahohin Najeriyar dake fama da tashe-tashen hankula da ke alaka da kungiyar nan ta masu kaifin kishin addinin musulunci ta Boko Haram.

Jami'an tsaro masu aikin tabbatar da zaman lafiya a jahar sun ce sun dauki matakan tsaro.