Mutane sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Benue

Kananan jiragen ruwa a Nijeriya
Image caption Kananan jiragen ruwa a Nijeriya

Ma'aikatan ceto a tsakiyar Najeriya na can na laluben gawarwakin wasu mutane kimanin hamsin da suka nutse a ruwa bayan da jirgin ruwan da suke tafiya ciki ya kife a kogin Buruku da ke jihar Benue.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda a jihar ya shaidawa BBC cewa ya zuwa yanzu dai gawarwaki goma sha bakwai ne aka samu.

Jirgin dai ya kife ne shekaranjiya Alhamis da daddare amma sai a jiya Jumu'a zuwa yau Asabar ne ake samun bayanai game da lamarin.