Masar: An yi arangama da ɗalibai

Image caption Masar ta na fuskantar tashin hankali tun daga bara

Ɗalibai magoya bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka haramta a Masar sun yi arangama da 'yan sanda a jami'ar Al-Azhar a birnin Alkahira.

Jami'an tsaro sun ce daliban sun yi kokarin hana wasu 'yan ajinsu zama su zana jarabawa ne.

Daliban sun kuma cinna wuta a sashen nazarin kasuwanci, sai 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.

Akwai kuma rahotannin cewa wuta ta tashi a sashen nazarin ayukan noma na jami'ar.

An dai kashe dalibi guda a tashin hankalin.