Lebanon ta harba makamai arewacin Isra'ila

Image caption Rundunar Sojin Isra'ila ta ce ta maida martani

Wasu makaman roka biyu da aka harba daga Labanon sun fashe a arewacin Kasar Isra'ila.

Makaman sun sauka ne kusa da garin Kyriat Shmona, amma ba su jikkata kowa ba, ko kuma janyo wani ta'adi.

Rundunar Sojin Isra'ila ta ce ta maida martani ta hanyar harba makamin atilare.

Iyaka tsakanin Kasashen biyu ta dan yi shiru tun yakin shekarar 2006 da aka gwabza tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Amma zaman dar-dar ya karu a makonni biyun da suka gabata, a lokacin da wani dan Lebanon ya kashe wani sojin Isra'ila har lahira a lokacin da yake tuka mota.

Karin bayani