Za a tantance yawan dakarun Machar a Bor

Reik Machar
Image caption An bada rahotan matasa na jerin gwano a Bor

Majalisar dinkin duniya ta ce za a yi amfani da jirage a yau lahadi domin kokarin tantance yawan matasan da aka bada rahotan sun yi jerin gwano a garin Bor.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce dubban matasa masu marawa tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar bayana sun yi jerin gwano a garin Bor.

Kakakin hukumar wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta kudu Joe Contreras ya shaidawa BBC cewa fitowar matasan na da hadarin gaske.

Sai dai kakakin 'yan tawaye ya musanta alakar tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar da matasan.

Karin bayani