Reshen APC na Sokkoto ya gargadi jam'iyya

Image caption Rikicin sabuwar jam'iyyar APC a Sokkoto ya dauki sabon salo

Ga alamu dai rikicin da ya kunno kai a sabuwar jam'iyyar APC a jahar Sakkwato ya dauki sabon salo.

Bangaren da ke goyon bayan tsohon gwamnan jahar Attahiru Bafarawa ya gargadi shugabannin jam'iyyar na kasa da su yi nesa da reshen jam'iyyar na jahar.

Shugabannin tsoffin jam'iyyun ANPP da ACN da kuma CPC da suka dunkule zuwa jam'iyyar ta APC sun ce sune suka cancanci shugabancin jam'iyyar a Sokkoto.

Shugabannin tsoffin jam'iyyun uku sun kuma sake jaddada goyon baya ga tsohon gwamnan jahar Sokkoto Attahiru Bafarawa.