Bangui: Dubban mutane sun nemi mafaka

Rikici a kusa da birnin Bangui
Image caption Rikici a kusa da birnin Bangui

Kungiyar agajin likitoci ta Medicin San Frontieres ta ce, fiye da mutane dubu dari da fadan addini ya raba da muhallinsu a jamhuriyar tsakiyar Afurka suna zaune ne a wani sansanin wucin-gadi dake kusa da babban filin jirgin saman kasar , a birnin Bangui.

Hare-haren da dakarun 'yan tawayen Seleka, wadanda musulmi ne da suka kwace mulki cikin watan Maris, da kuma hare-haren sojan sa kai Krista ya haddasa mutuwar mutane fiye da dubu.

Lamarin ya kuma raba mutane da dama da muhallinsu.

A yanzu haka hukumomin Nijeriya na kokarin kwashe dubban 'yan kasar dake zaune a can.