An kama ma'aikatan Al-Jazeera a Masar

Al Sisi
Image caption An ce 'yan jaridar Al Jazeera sun tattauna da 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi

Hukumomin kasar Masar sun kama ma'aikatan gidan talabijin din Al-Jazeera su Uku.

Ministan harkokin cikin gidan na kasar yace 'yan jaridar sun tattauna da mambobin Kungiyar 'yan uwa Musulmi ba bisa ka'ida ba wadda aka ayyana matsayin kungiyar 'yan ta'adda a makon da ya wuce.

Ya kara da cewa Al-jazeera na watsa labaran da suke barazana ga tsaron kasar, an kuma kwace kayan aikin 'yan jaridar da suka hada da na'urar daukar hoto data nadar magana.

Sojoji sun hanbarar da gwamnatin Mohammad Morsi da ya kasance dan kungiyar 'yan uwa a watan Yulin wannan shekarar.

Karin bayani