Schumacher na cikin mawuyacin hali

Shumacher
Image caption Shumacher ya samu rauni a kansa

Tsohon babban dan wasan tseren motoci na Formula one, Micheal Schumacher ya na cikin mawuyacin hali a asibiti, bayan ya samu mummunan rauni a kansa.

Bayanan da suke fitowa daga likocin birnin Guronoble na cewa an kawo Mr Shumacher cikin halin rai kwakwai-mutu kwakwai kuma ana bukatar yi masa aiki na gaggawa saboda ciwon da ke kansa.

Wani kwararren likitan kwakwalwa a Fransa kuma babban aboki ga Mr Shumacher ya isa asibitin.

Matukin ya na sanye da hular kwano a lokacin da ya yi hadarin,kan sa kuma ya daki wani dutse da ke gefen titi kusa da wurin shakatawa na Meribel, sai jirgin Helicopter ne ya dauke shi zuwa asibiti.