Bom ya kashe mutane 15 a Rasha

Image caption Masu bincike sun bayyana harin da cewar na ta'addanci ne

'Yan sanda a Rasha sun ce wani harin bom ya sake tashi a cikin wata babbar motar safa a garin Volgograd da ya hallaka mutane akalla goma sha biyar.

Tashin bom din ya zo ne kwana daya kacal bayan wani harin kunar bakin wake ya hallaka mutane goma sha bakwai a tashar jirgin kasa da ke garin.

Masu bincike sun bayyana harin din da aikin ta'addanci kuma sun fara gudanar da bincike dan gano bakin zaren.

Duka hare-haren biyu dai sun janyo damuwa kan matsalar tsaro, kasan cewar za a fara gasar wasannin Olympics a watan Fabrairun shekara mai zuwa a kasar Rasha.

Karin bayani