'Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 56'

Image caption Jihar Borno na karkashin dokar ta baci

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram akalla 56 a lokacin da ta kai hare-hare ta sama da kasa a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojan, Captain Aliyu Danja, wanda ya bayyana haka a wata sanar da ya fitar, ya kara da cewa an raunata sojoji biyu lokacin da suka kai hare-haren a gandun dajin Alafa da ke jihar Borno ranar Asabar.

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin.

Hakan na faru ne a daidai lokacin da 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kashe mutane 12 tare da raunata wasu da dama a harin da su ka kaddamar a kauyuka biyu da ke jihar Borno.

Sau da dama dai sojin Nigeria na cewa suna kashe 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram.

A makon jiya ne dai shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, a wani bidiyo ya ce kungiyarsu ce ta kaddammar da hari a kan barikin sojoji da ke garin Bama a jihar Borno.

Kawo yanzu hukumomin tsaro a kasar ba su ce komai a kan al'amarin ba.

Karin bayani