Congo: An kashe 'yan bindiga 40

Image caption Akwai dubban sojojin kiyayen zaman lafiya a Kinshasa

Dakarun gwamnati a Kinshasa, babban birnin Congo sun kashe mutane arba'in sakamakon arangama da wasu 'yan bindiga da suka tada zaune tsaye a birnin.

Rahotannin sun ce sojojin sake kwace iko da kafofin yada labaran hukuma, bayan harin da gungun matasan dauke da makamai su ka kai, ya haddasa dakatar da watsa shirye-shirye.

Wani mai magana da yawun gwamnati na cewa a yanzu al'amurra sun lafa a birnin na Kinshasa, bayan da aka tura dakarun tsaro domin su shawo kan wasu hare haren biyu a babban filin jirgin saman kasar, da kuma wani barikin soja.

A shekarar 1997, dakarun kasar tare da goyon bayan na Rwanda suka hambarar da gwamnatin Mobutu Sese Seko suka saka Laurent Kabila wanda aka kashe kuma dansa Joseph Kabila ya dare kan mulki.

Karin bayani