Isra'ila ta sako fursunonin Palasdinawa 26

Fursunonin Palasdinawa
Image caption Wadannan sune fursunonin da suka jima a hannun Isra'ila

Isra'ila ta sako fursunoni Palasdinawa su 26 da suka dade a gidan kaso a karkashin wata yarjejeniya da kasar Amurka ta shiga tsakani domin dawo da tattaunar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Wadannan su ne kashi uku na fursunonin da Isra'ila ta saka, da yawancinsu ake tsare da su tun kafin a sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo a shekarar 1993

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas, ya jagoranci bikin yiwa fursunonin murnar sakin su.

Ana kuma sa ran za a sako kashi na karshe na fursunonin a watan Aprilun shekara mai zuwa.

Karin bayani