Babu maganar kafa gwamnatin hadaka- Kiir

Shugaba Kiir da shugaba Museveni
Image caption Shugaba Museveni ya yi barazanar amfani da karfi a kan Riek Machar

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya kawar da yiwuwar kafa gwamnatin hadaka da jagoran 'yan tawaye Riek Machar, a kokarin kawo karshen rikicin kabilancin da ya hadasa mutuwar dubban mutane.

Shugaba Kiir ya shaidawa BBC cewa bai kamata a saka wa Mr Machar ba ta hanyar sa shi a gwamnatin hadaka ba, saboda ya yi tawaye .

Haka nan shugaba Kiir ya ki sakin fursunonin siyasa magoya bayan abokin hamayyar tasa.

Shi kuma Mr Machar ya kekasa kasa cewar, ba zai yi wata tattaunawa ba, sai an sako mutanen nasa.

A halin da ake ciki kuma, shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni , wanda ya je Sudan ta Kudu, a kokarin kulla 'yarjejeniyar sulhu, ya yi barazanar amfani da karfi a kan Riek Machar idan ya ki bada hadin kai.

Karin bayani