Amurka za ta ba Rasha hadin kai ta fuskar tsaro

Ta'adin da aka yi a Volgograd
Image caption Amurka ta ce za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro a Sochi

Amurka ta yi wa Rasha tayin ba ta cikakken hadin kai ta fuskar tsaro a shirye shiryenta na karbar bakuncin gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu, bayan hare- haren kunar bakin wake biyu a birnin Volgograd.

Kakakin Fadar White House, Caitlin Hayden, ta ce Amurka za ta yi marhabin da duk wata dama ta taimakawa wajen tabbatar da tsaron lafiyar 'yan wasa da kuma 'yan kallo a wasannin na Olympic na hunturu da zaa yi a Sochi, wadanda zaa fara a ranar 7 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Hakazalika Ms Hayden ta ce Amurka ta yi Allah waddai hare-haren da aka kai a Volgograd, tare da mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayikansu.

Mutane akalla talatin-da-daya ne suka mutu a hare haren bam din, a babbar tashar jirgin kasar birnin, da kuma a cikin wata motar bus dake cike da pasinjoji.

Wakilin BBC ya ce ana zargin cewa wasu 'yan kishin Isalama ne daga yankin Caucasus na kasar ta Rasha suka kai hare haren , domin kawo cikas ga Wasannin na Olympic.

Karin bayani