PDP: Geidam ya maida wa Ngama martani

Image caption Gwamna Ibrahim Geidam na jihar Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta maida martani game da kalaman minista a ma'aikatar kudi ta Najeriya, Alhaji Yarima Lawal Ngama ya yi game da zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar a karshen mako.

Ministan ya yi zargin cewar jam'iyyar APC mai mulki ta rubuta sakamakon zabe ne kawai, saboda a cewarsa dokar kasar ba ta amince a gudanar da zabe a karkashin dokar ta baci ba.

Kakakin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam wato Malam Abdullahi Bego ya ce babu gaskiya a kalaman ministan saboda a cewarsa masu sa'ido daga jihohi daban daban na kasar sun yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewar jam'iyyar APC mai mulkin jihar ce ta lashe kujerun shugabannin duka kananan hukumomin jihar da kuma na kansiloli.

Karin bayani