Ba ni da lafiyar komawa aiki - Inji Suntai

Gwamna Danbaba Dan fulani Suntai
Image caption Gwamna Danbaba Dan fulani Suntai na Jihar Taraba

A cikin wani vidiyo da ya bayyana a shafin Internet na YouTube wani da ake cewar gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai ne ya bayyana cewa, ba shi da koshin lafiyar da zai koma kan mukaminsa.

Gwamna Danbaba Suntai dai yayi hatsarin jirgin sama ne a shekara ta 2012, lamarin da ya kai shi doguwar jinya a Jamus da kuma Amurka.

Batun ko Gwamna Danbaba yana da koshin lafiyar da zai iya komawa kan mulki shi ne ya mamaye siyasar jihar Taraba cikin.

Koda a cikin yan kwanakin nan dai an yi baza labarin cewar wasu na kusa da gwamna Suntai na ta kokarin ganin sun mayar da shi kan karagar mulki, abunda ya hada da kai shi ga Shugaba Goodluck Jonathan don ya taimaka masa kan wannan bukata ta su.