Sojin Iraqi na kai farmaki a Fallujah

'Yan bindiga a Fallujah
Image caption 'Yan bindiga a Fallujah

'Yan Iraqin dake zama birnin Fallujah na lardin yammacin kasar na Al-Anbar sun sheda wa BBC cewar iyalai na ta tudada zuwa kauyuka makwabta da kuma birane domin tsere wa ruwan bindigogin atilere da kuma hare hare ta sama da soji ke yi.

Farmakin ya biyo bayan karfafa ikon da mayakan kabilu da 'yan gwagwarmayar kungiyar Al-Qaida suka yi ne a birnin.

Kwamandan yanki na sojin ya shedawa kafofin watsa labarai na gwamnatin Iraqi cewar za a dauki 'yan kwanaki kafin a kawar da 'yan gwagwarmayar masu alaka da Al-Qaida daga muhimman birane 2 na lardin, Fallujah da Ramadi.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce gwamnatin Amurka za ta samar da taimako ga dakarun Iraqi a yakin da suke , amma ba za ta tura dakarun Amurka ba.