Najeriya ta cika shekaru 100 da kafuwa.

Map din Najeriya
Image caption Map din Najeriya

A yau ne Najeriyar ke cika shekaru dari cif-cif a matsayin kasa daya dunkulalliya, bayan da turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka hada lardunan kudanci da na arewacin kasar a shekarar 1914, ka na aka baiwa kasar su na Najeriya.

Bayan samun 'yanci a shekarar 1960, kasar ta yi fama da yakin ba-sa-sa sakamakon yunkurin ballewa da yankin kudu maso gabashin kasar wato yankin Biafra ya yi a shekarar 1967 amma duk da hasashen da wasu su ka sha yin na cewa kasar zata wargaje, har yanzu kasar ta na nan dunkulalliya ko da yake akwai wasu kalubale da dama da take fuskanta.

Mazauna kasar dai sun bayyana ra'ayoyin su dangane da matsayin Najeriyar a yanzu.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba