Ƙazafi: Za a yi wa wani bulala 80

Image caption Shams, mawakiyar da ake zargin an yi wa ƙazafi

An bayar da rahoton cewar an yanke wa wani mutumin Saudiya hukuncin bulala 80 da kuma daurin watanni a gidan yari saboda zargin aikata lalatar da yayi wa wata fitacciyar mawakiya.

Mutumin dai ya yi wa fitacciyar mawakiyar ta yankin Gulf zargin ne ta kafar sadarwa ta Internet.

Mawakiyar Shams, ta shedawa wata jaridar kasar cewar ta kai batun kotu ne domin kare mutunci ƙimarta.

Ta ce zargin wanda ya hada da hotunan karya za su iya kai ga a kashe ta.