Ana aikata ta'asa kan fararen hula a Sudan ta Kudu

Rikicin Sudan ta Kudu
Image caption Rikicin Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai kwararan shaidun da suka nuna aikata ta'asa kan fararen hula da sojojin da aka cafke a rikicin Sudan ta Kudu.

Majalisar Dinkin Duniyar na fatan tattaunawar sulhun tsakanin bangarorin biyu masu rikici da juna a kasar Habasha za ta haifar da gaggauta tsagaita wuta.

Sai dai rikicin ya kara ta'azzara kana dakaru masu goyon bayan jagoran 'yan tawaye Riek Machar suka kwace ikon birnin Bor.

Shugabannin kasashen gabashin Afrika sun gargadi Mr Machar cewa zasu tsoma baki, matukar ya ki amincewa da shiga tattaunawar sulhu da abokin gabar tasa shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu.

Ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu Barnaba Marial Benjamin ya shaidawa BBC cewa har yanzu babu batun tsagaita wuta dakarun, ya ce Mr Machar na ta kai hari a garin Bor dake karkashin ikon gwamnatin jamhuriyar Sudan ta Kudu.

Akalla mutane dubu daya ne aka hallaka a rikicin Sudan ta Kudun cikin makonni biyun da suka gabata.