Sudan ta Kudu: An yi kiran a tsagaita wuta

Image caption Mutane da dama suna cikin wani hali a Sudan ta kudu

Dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya a Sudan ta kudu sun yi kiran a kawo karshen fadan da ake yi a kasar.

Ya zuwa yanzu dai gwamnati da 'yan tawaye sun amince su aika wakilai zuwa taron sulhu da za a yi a Ethiopia.

Sai dai kuma har yanzu 'yan tawaye ba su amince sun tsagaita wuta ba.

Hilde Johnson jagorar ayukan majalisar dinkin duniya a Sudan ta kudu ta nanata kira ga ɓangarorin dake fada da juna su ajiye makamai.

Tsagaita wuta dai zata taimaka wajen baiwa ma'aikatan agaji damar kai ɗauki ga sassan da yanzu haka ake fafatawa.