Ana bata kashi a birnin Fallujah na Iraki

Image caption Dakarun gwamnati na fafatawa da 'yan bindiga

Zaratan sojojin Iraki, na fafatawa da masu fafutika na wata kungiya mai alaka da Al Qaida a birnin Fallujah inda masu fafutikar suka kwace iko da wasu sassa na birnin.

Masu fafutika na kungiyar kasar Musulunci ta Iraqi, sun kwace iko ne da akalla ofisoshin 'yan sanda 10, kuma sun saki fursunoni da dama tare da kakkafa wuraren binciken ababen hawa a kan hanyoyin dake shiga Fallujah da kuma cikin garin.

Wakilin BBC ya ce Kwamandan zaratan sojojin na Iraki, ya ce yanzu haka ana mummunan dauki ba dadi tsakaninsu da masu fafutikar da nufin kwato iko da wuraren da masu fafutukar suka kama.

An soma tashin hankalinne a ranar Litinin, bayan da jami'an tsaro suka tarwatsa wasu masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a birnin Ramadi mai makwabtaka, suna masu korafin cewa gwamnati ba ta yi wa 'yan Sunni adalci.

Karin bayani