Hezbollah ta yi kiran a samu hadin kai Lebanon

Fashewar Bam
Image caption Fashewar Bam

Mataimakin shugaban kungiyar fafutuka ta Hezbollah a Lebanon ya yi kiran da'a samu hadin kai domin kaucewa rusa kasar.

Wannan jawabi na sa Sheikh Na'im Kassim ya zo ne bayan fashewar wani bam da aka dana cikin mota wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla hudu a unguwar da 'yan Shi'a ta Hezbollah ke da karfi a Beirut babban birnin kasar.

Fiye da mutane sittin sun samu raunuka a harin.

Sheikh Na'im ya ce an yi niyyar wargatsa kasar ne a saboda haka ya yi bayani akan bukatar da ke akwai ta fahimtar siyasa.

Kasar Labanon dai ta fuskanci tashin bama-bamai, yayinda tashin hankali ke karuwa a makwabciyarta Syria.

Ko a makon da ya gabata wani bam da ya tashi ya hallaka wani tsohon ministan kasar Mohd Chatah, kisan da magoya bayansa suka dora alhaki akan Kungiyar Hizbullah da kuma gwamnati.