Ministan tsaron Faransa ya kammala ziyara a Nijar

Shugaban kasar Nijar Mamadou Issoufou  da na kasar Faransa
Image caption Shugaban kasar Nijar Mamadou Issoufou da na kasar Faransa

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya kammala ziyararsa a Nijar inda ya gana da shugaban kasar, Alhaji Muhammadu Isssofou a birnin Yamai.

Ministan tsaron Faransan dai yana ziyara ne a kasashen yankin Sahel, inda ake fuskantar barazanar ayyukan 'yan ta'adda.

Kafin Niger dai ministan ya ziyarci Mali, inda dakarun Faransa ke aikin samar da zaman lafiya.

Tun dai barkewar rikicin kasar Mali ne da matsayin da kasar Nijar ta dauka dangane da hanyoyin magance shi, kasar ta zama babbar kawa kuma abokiyar shawara ga manya-manyan kasashen duniya musamman Faransa, dangane da yadda za a inganta tsaro a yankin Sahel.

Bayan ganawar da yayi da shugaban kasar ta Nijar Ministan tsaron na Faransa ya shaidawa manema labarai cewa tuni ya gana da dakarun kasarsa dake Mali da Nijar, kana zai wuce kasar Chadi domin ganawa da takwarorinsu.

Ya ce babban burin shine a karbewa dukkanin bangarorin da ke gaba da juna makaman su, don maido da zaman lafiya a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda daga nan za a kai ga kafa hukumomin wucin gadi a kuma cimma shirya zabubbuka a cikin wannan shekarar.