An haramta bara a jihar Filato

Image caption Gwamna Jonah Jang na Filato

Gwamnatin jihar Filato a Nigeria ta haramta bara a kan tituna musamman a Jos babban birnin jihar ba tare da bata lokaci ba.

A cewar gwamnatin ta dauki matakinne saboda dalilai na tsaro.

Jihar Filato itace ta baya-bayanan da ta dauki wannan matakin na haramta bara-barace a kan tituna.

Jihohin musamman a kudancin kasar tuni suka haramta bara, kuma su ka tasa keyar ma barata zuwa jihohinsu na asali.

A jihar Kano dake arewacin kasar ma, majalisar dokoki ta amince da kudurin dokar hana bara a kan titi.

Karin bayani