Sharon na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai

Image caption Ariel Sharon

Likitocin dake jinyar tsohon Firaministan Isra'ila, Ariel Sharon, sun ce yanayin da yake ciki ya kara tabarbarewa, kuma komai na iya faruwa.

Likitocin sun ce muhimman sassan jikinsa da dama sun samu matsaloli, kuma iyalansa suna tare da shi a gadon asibiti.

Daya daga cikin likitocin Farfesa Zeev Rotstein ya ce "Akwai alamun tabarbarewa a halin da Mr Sharon yake ciki, inda wasu sassan jikinsa suka daina aiki yadda ya kamata, ciki har kodarsa".

Mr Sharon mai shekaru 85 da haifuwa, ya kasance cikin yanayin doguwar suma, bayan ya yi fama da bugun zuciya a shekara ta 2006.

A ranar Laraba ne, likitocin suka ce halin da Mr Sharon din yake ciki ya kara munana.

Karin bayani