Mutane na bukatar agaji a Sudan ta Kudu

'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
Image caption 'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu

Kungiyoyin agaji sun ce dubun dubatar mutanen da rikicin Sudan ta Kudu ya tilastawa barin gidajensu na bukatar taimako matuka.

Akasarin su sun gudu zuwa sansanonin dake gabar tekun Nilu, don tsira daga fadan da ya rincabe a birnin Bor tsakanin magoya bayan shugaba Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Shugaban Kungiyar agajin Likitocin sa kai na Medicins Sans Frontieres ya ce babu tsaftataccen ruwa a sansanin, mutane na shan gurbataccen ruwa daga kogin Nilu, suna kuma yin ba haya a fili saboda rashin makewayi wanda ke nuna barazanar yiwuwar barkewar cutar gudawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta shaidawa bangarorin biyu dake yakar juna a Sudan ta Kudun cewa sun kai ga makura, amma kuma har yanzu za su iya ceton kasar.

Bangarorin biyu dai na shirin zaman tattaunawar sulhu ne a kasar Habasha, amma kuma har yanzu ana ci gaba da gwabza fadan.