Harbe-harbe a Filin jirgin saman soji a Congo

Sojojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congp
Image caption Sojojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congp

Jami'ai a Congo sun ce an danyi wani harbe-harbe na takaitaccen lokaci a filin jirgin saman soji na Ndolo da ke kusa da Kinshasa babban birnin kasar.

Sai dai kuma ba a samu rahoton samun rauni a harbe-harben ba, yayin da ba kuma gano wadanda suka aikata hakan ba.

Wannan harin dai yazo ne kwanaki kadan bayan da wasu matasa dauke da makamai su ka farwa filin jirgin sama da gidan talbijin da kuma barikin soji na kasar .

An bada rahoton cewa, matasan magoya bayan wani mutum ne da ke da'awar shi mai bushara ne wato Joseph Mukungubila wanda ya ke sukar shugaba Joseph kabila.

Sai dai kuma dakarun Congon sun kashe maharan da dama.