An kai hari gidan yarin Guerrero a Mexico

Gidan yarin Mexico
Image caption Gidan yarin Mexico

Dakarun Mexico da kuma 'yan sandan kasar sun karbe ikon kula da wani gidan yari da ke kudu maso yammacin Mexico bayan arangamar da akayi.

An yi arangamar ne tsakanin masu gadin gidan yarin da kuma wasu 'yan bindiga shida lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane tara.

Ofishin babban mai shari'a na kasar ya ce, 'yan bindigar sun samu damar shiga gidan yarin ne da ke jihar Guerrero ta hanyar batar da kama inda suka je a matsayin jami'ai na musamman.

Bayan shigar ta su ne suka bude wuta akan wasu fursunoni har suka kashe hudu daga cikin su.

Jin hakan ya sa masu gadin wajen suka shiga anan ne suka kashe 'yan bindigar biyar.

Har yanzu dai ba'a san dalilin kai harin ba.