Iraqi: 'Yan bindiga sun ƙwace iko da Fallujah

Rahotanni daga Iraqi sun ce, gwamnatin tarayyar ƙasar ta rasa iko da birnin Fallujah na yammacin ƙasar.

Wata majiyar tsaro ta shedawa BBC cewar wani gungun 'yan gwagwarmaya dake da alaƙa da kungiyar Al-Qaida, wato kungiyar kasar Musulci ta Iraqi da Syria ce ke iko da kudancin birnin.

Wani ɗan jarida na Iraqi a Fallujah, Mohammed Abdullah, ya shedawa BBC cewar 'yan kabila tare da ƙungiyar mai goyon bayan Al'Qaida na iko da sauran birnin.

Ya kuma ce 'yan bindigar sun fatattaki 'yan sanda da sauran jami'an tsaro.

Pirayim Minista Nouri Al-Maliki ya ce soji ba za su ja da baya ba har sai sun kawar da dukkanin ƙungiyoyin 'yan gwagwarmaya a lardin.