Bangladesh: Ana zaɓe, an kashe mutune 11

An kashe aƙalla mutane goma sha ɗaya yau yayin da aka soma zaben kasa baki ɗaya a Bangladesh inda, zaben yake fuskantar turjiya da matuƙar adawa.

Mutane ƙalilan ne dai suka fito jefa kuri'a.

Jam'iyyar Bangladesh Nationalist Party da ƙawayenta suna ta ƙoƙarin gamsar da jama'a kada su fito jefa kuri'a.

Suna yin hakan ne dai saboda Praminista, Sheikh Hasina ta ki amincewa da bukatarsu cewa, ta sauka daga mukaminta kafin zaben.

An dakatar da yin zaben a mazabu dari da hamsin.