Iraqi ta rasa wani yankinta ga ISIS

Iraqi na kokarin murkushe masu gwagwarmaya a Fallujah
Bayanan hoto,

Iraqi na kokarin murkushe masu gwagwarmaya a Fallujah

Rahotanni daga Iraqi na cewa gwamnatin kasar ta rasa iko da birnin Fallujah da ke yammacin kasar ga masu gwagwarmaya dake da alaka da Alqaeda wadanda ake wa lakabi da ISIS.

Shugaban 'yan sandan yankin Anbar Hadi Razeji ya ce mutanen sun mamaye birnin na Fallujah kuma yanzu haka al'ummar birnin baki daya sun zama fursunonin kungiyar ta ISIS.

Fada ya barke ne bayan da wasu dakarun soji suka balle suke zanga-zangar kin jinin gwamnati a sansanin birnin Ramadi mai nisan kilomita hamsin a yammacin Fallujah.

Mr Al-Maliki ya zargi masu gwagwarmayar ne da ayyana kasa mai zaman kanta a Anbar da abinda ya kira tallafin wata kasa a yankin tekun Gulf da bai bayyana sunanta ba.