An fara tattaunawar sulhu kan Sudan ta kudu

Image caption Ana saran kawo karshen rikicin Sudan ta kudu

Bangarori biyu da ke rikici da juna a Sudan ta Kudu sun fara tattaunawar da za ta kawo karshen tashin hankalin da kasar ke ciki na makwanni.

Taron dai ana gudanar dashi a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha bayan wani jinkiri na bazata.

Sai dai wakilin 'yan adawa Tabang Deng ya shaidawa BBC cewa shugaba Salva Kiir shi ya kamata ya fara daukar matakin kawo karshen rikicin.

Deng yace, "da irin kisan kare dangin da ake yi a kasar nan da fursunonin siyasa da ake tsare da su, ba ta yadda za a yi a samu damar zama teburin sulhu."

A yau Lahadi ne za a soma tattaunawar ta kai tsaye tsakanin wakilan Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Karin bayani