Sudan ta Kudu: Ana gwabza faɗa a Bor

Yayin da tattaunawar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu ke samar da wani ɗan ci gaba, ana gwabza ƙazamin faɗa domin karɓe iko da muhimmin garin nan na Bor.

An kashe wani Janar din soji a fadan, yayin da ake iya ganin gawarwaki da kuma ƙonannun tankokin yaƙi a kan titin zuwa Bor.

Tuni dai garin na Bor ya sauya hannu har sau uku tsakanin 'yan tawaye da kuma gwamnati.

Editan BBC kan harkokin Afrika ya ce kowanne ɓangare ga alama na son samun galaba mai dama a filin daga kafin yiwuwar tsagaita buɗe wuta.

Wakilin kasar Ethiopia na musamman a Sudan ta Kudu, Seyoum Mesfin, yayi gargadin cewar idan tattaunawar ta ci tura, to kowanne ɓangare zai ji a jikinsa.