ISIS ta rasa ikon wasu yankuna a Syria

Image caption ISIS ta gwamza fada da abokan hamayyarta a Syria

Rahotani na nuni cewar kungiyar masu gwagwarmaya ISIS ta rasa iko da wasu yankunan da ke hannunta a fadan da ta gwabza da abokan hamayyarsu na Syria.

Kungiyar ta bada wa'adin tsagaita bude wuta a garin Atareb inda rahotanni ke cewa ta rasa iko da shi.

Kakakin kungiyar ya ce idan ba a tsagaida wuta a garin ba za ta dakatar da kai hare-hare akan sojojin gwamnati a garin Aleppo.

Masu gwagwarmayar da dama an rawaito an kashe su ko kuma an kamasu.

Karin bayani