Al-Bashir ya ziyarci Sudan ta Kudu

Image caption Shugaban Sudan Omar al-Bashir na kokarin sasanta rikicin Sudan ta Kudu.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, na tattauna wa da shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu a Juba, babban birnin kasar game da rikicin da ke ci gaba da faruwa a kasar.

Sudan ta ce ta na goyon bayan sasanta rikicin da ya raba dubunnan daruruwan mutane daga matsugunnansu.

Tattalin arzikin Sudan dai ya dogara ne kan man fetur da ake fitarwa ta yankinta daga Sudan ta Kudu, wacce ta samu 'yancin kai a 2011.

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, wanda zai gana da wakilan gwamnatin da 'yan tawayen a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia ya bukaci a tsagaita wuta.